logo

HAUSA

Gwamnan jihar Kaduna: Ba ’yan Najeriya ne kadai ke fama da matsalar tsadar rayuwa ba, abun ya shafi duniya baki daya

2024-02-20 10:16:41 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya Sanata Uba Sani ya ce, ba ’yan Najeriya ne kadai suke fuskantar matsalolin rayuwa ba, al’amarin ya shafi duniya ne baki daya saboda sauye-sauyen tattalin arziki.

Gwmnan ya tabbatar da hakan yayin firarsa da manema labarai a birnin Abuja, ya ce, bai kamata a rinka dorawa mutum guda laifin matsalar da yanzu haka ’yan Najeriya ke ciki ba, amma ya ce akwai mafita.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gwamnan na jihar ta Kaduna ya ci gaba da cewa, ba sabon abu ba ne a tarihin kasashe, a sami koma bayan tattalin arziki wanda yake haifar da matsin rayuwa ga ’yan kasa.

Ya ce, kasashe da suka fi Najeriya karfin tattalin arziki a duniya suna tsintar kansu a irin wannan hali, to amma kuma ana fita daga mawuyacin hali ne idan gwamnati da al’umma sun hada kai tare kuma da nuna kishin kasa da kuma dabbaka zaman lafiya da fahimtar juna.

Ya bada misalin cewa, ko a kwanan nan tattalin arzikin kasar Burtaniya ya sami koma baya matuka, inda al’ummar kasar suka fuskanci tsadar kayayyakin masarufi.

Sanata Uba Sani ya ci gaba da cewa, hakika gwamnatin tarayyar Najeriya na bakin kokarinta tun da tana turawa ma’aikatu da sauran hukumominta kudaden gudanar da ayyukan raya kasa, a don haka wajibi ne irin wadannan hukumomi su yi kokarin yin abin da ya kamata da kudaden domin ’yan kasa su sami walwala yadda ya kamata.

Ko da yake dai gwamnan na jihar ta Kaduna ya kawo shawarar cewa akwai wasu matakai da ya kamata a bi muddi dai ana son a ci karfin matsin rayuwa da al’ummar kasar ke ciki a yanzu haka.

“Abin da ya kamata a yi a wannan matsanancin yanayi, shi ne a zauna a duba rawar da kananan hukumomi za su taka domin kuwa kananan hukumomi suna da muhimmancin gaske wajen tabbatar da ganin kudaden da ake turo musu yana isa kai tsaye ne ga mutanen da suke zaune a yankunan karkara.” (Garba Abdullahi Bagwai)