logo

HAUSA

Ziyarar Wang Yi Ta Nuna Kwanciyar Hankali A Hadin Gwiwar Sin Da Sifaniya

2024-02-20 19:46:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Talata cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai kasar Sifaniya ta samu nasara, ita kuma ta nuna yadda ake samun daidaito bisa manyan tsare-tsare a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Mao ta shaidawa taron manema na yau da kullum cewa, duk da sauye-sauyen yanayin duniya, kasashen biyu sun kasance suna kiyaye al'adar mutuntawa da amincewa da juna, tafiyar da juna bisa daidaito da yin hadin gwiwar samun nasara tare, da raya dangantaka da tsayayyun manufofin sada zumunta, da goyon bayan muhimman muradun juna da manyan batutuwan dake shafar juna.

A yayin ziyarar, bangarorin biyu sun jaddada aniyarsu ta kara bude kofa ga juna, kana sun amince da kara yin hadin gwiwa a fannonin sadarwa, da kiwon lafiya, ababen hawa masu amfani da wutar lantarki da makamashi mara gurbata muhalli

Bangarorin biyu sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare, don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar Sin da EU, don kara samar da kwanciyar hankali a duniya mai cike da tashin hankali.(Ibrahim)