logo

HAUSA

Tsibirin Huangyan da yankunan tekun dake kewayensa mallakar Sin ne

2024-02-19 20:21:46 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, game da batun ra’ayin jami’in kasar Philippines kan tsibirin Huangyan, Sin ta jaddada cewa, tsibirin Huangyan da yankunan tekun dake kewayensa mallakar kasar Sin ne.

Rahotanni na cewa, kakakin hukumar kula da kamun kifi da albarkatun ruwa ta kasar Philippines ya bayyana a ranar 17 ga wannan wata cewa, masunta na kasar Sin suna amfani da sinadarin cyanide a tsibirin Huangyan don lalata wuraren kamun kifi na kasar Philippines.

Game da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, lamarin da bangaren Philippines ya fada, ya kirkire shi ne da gangan. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhallin halittu da tabbatar da albarkatun kifi, tare da dagewa wajen dakile kamun kifi ba bisa ka'ida ba. (Zainab)