logo

HAUSA

Al’ummar Afirka ta yi maraba da sakon Xi Jinping ga taron AU karo na 37

2024-02-19 13:54:47 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron kungiyar Tarayyar Afrika (AU) karo na 37 a ranar 17 ga wata, sakon da aka yi maraba da shi sosai a nahiyar.

Jama’a daga kasashen Afrika daban-daban na ganin cewa, sakon ya nuna yadda Sin ta dauki dangantakarta da Afrika da muhimmanci da kuma goyon baya mai karfi da take ba ci gaban nahiyar da farfadowarta.

Sun kuma yi ammana cewa dangantakar bangarorin biyu za ta ci gaba da kasancewa tubalin hadin gwiwar kasashe masu tasowa da ma na hadin gwiwar Afrika da sauran kasashen duniya, haka kuma suna sa ran ganin bangarorin biyu sun samu ci gaba a tafarkin zamanantar da kansu. Tuni dai aka dauki matakai masu ruwa da tsaki wajen hada hannu domin gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya da samar da karin alfanu gare su. 

A cewar Amadou Diop, dan kasar Senegal mai fashin baki kan harkokin da suka shafi kasar Sin, hadin gwiwar Sin da Afrika misali ne na hadin gwiwar kasashe masu tasowa wanda ke taka muhimmyar rawa a harkokin duniya. Ya ce hadin gwiwar Sin da Afrika na kunshe da sabon ra’ayin huldar kasa da kasa na moriyar juna, kuma ya samar da karin kuzari da karin damarmakin ci gaba ga duniya.

Shi kuwa Cavins Adhil, masanin harkokin kasa da kasa na kasar Kenya, ya ce tun bayan hadin gwiwar shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, ababen more rayuwa a nahiyar Afrika sun samu ci gaban da ba a taba gani ba, lamarin da ya aza tubalin zamanantar da nahiyar da ma dunkulewarta. Ya ce shawarar raya duniya da ta tsaron duniya da ma ta jituwar mabambantan al’ummomi, wadanda kasar Sin ta gabatar, sun samu karbuwa a tsakanin kasashen Afrika. Ya ce al’ummar Sin da Afrika na da buri guda na samun ingantacciyar rayuwa. Kuma bisa la’akari da yanayinsu, Sin da Afrika za su yi aiki tare wajen samar da kyakkyawan muhallin cimma burikansu na ci gaba. (Fa’iza Mustapha)