logo

HAUSA

Bikin Bazara Na Shekarar Dabbar Loong Ya Baiwa Duniya Damar Ganin Muhimmancin Tattalin Arzikin Sin

2024-02-19 20:25:05 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, karuwar masu yawon bude ido na kasar Sin da na kasashen waje a lokacin bikin Bazara na shekarar dabbar Loong, ta sanya bikin Bazara ya zama kololuwar karuwar aikin yawon bude ido a duniya, da kuma baiwa duniya damar ganin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Alkaluma sun nuna cewa, a lokacin bikin Bazara, masu yawon bude ido na kasar Sin, sun kashe jimillar kudin da ya kai yuan biliyan 632.687, wanda ya karu da kashi 7.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2019, yawan kudaden da aka samu a fannin gidajen sinima na kasar Sin ya zarce yuan biliyan 8, lamarin da ya karya tarihi.

Mao ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga gudanar da mu'amalar mutane a tsakaninta da kasashen ketare, da ba da gudummawa ga kara bude kofa ga kasashen waje, da samar da yanayi mai kyau ga dukkan kasashen duniya, wajen raba damar da kasar Sin ke da ita. (Ibrahim)