logo

HAUSA

Sin Za Ta Ci Gaba Da Kiyaye Manyan Manufofinta Na Kasancewa Mai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali.

2024-02-19 20:09:40 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta gabatar da halartar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a gun taron tsaro na Munich karo na 60, yayin taron manema labaru da aka saba yi Litinin din nan, inda ta bayyana cewa, babban sakon da Wang ya gabatar shi ne cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye manyan manufofinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko da yaushe, a cikin duniya mai fama da tashin hankali

Mao ta ce, kamata ya yi hadin gwiwa da samun nasara tare, su zama tushen manufofin dukkan kasashe wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa. Kasar Sin tana son hada kai da dukkan bangarori, don samun nasara tare, da kaucewa hasara da dama, da kara tabbatar da tabbas a duniya, da samar da makoma mai kyau ga daukacin bil-Adama.(Ibrahim)