logo

HAUSA

Najeriya za ta samu dala biliyan 30 cikin tattalin arzikin ta daga masu saka jari ’yan kasa da na kasashen waje

2024-02-18 09:10:44 CMG Hausa

Ministan harkokin masana’antu, ciniki da zuba jari na tarayyar Najeriya Mrs. Doris Uzoka-Anite ta ce, manyan kamfanonin na cikin gida da na waje sun nuna sha’awarsu ta saka jari a Najeriya da ya kai na sama da dala biliyan 30.

Ministar ta tabbatar da hakan ne yayin taron manema labarai da ma’aikatar yada labarai ta kasar ta shirya a birnin Abuja. Ta ce tuni ma wasu kamfanonin suka fara saka jarin nasu a fannoni daban daban na ci gaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministar ta ce, tun watanni 8 da suka gabata gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shirye da masu saka jari, inda za su samar da wadannan biliyoyin dala cikin tattalin arzikin kasa ta hanyar aikace-aikace da kuma hada-hadar kasuwanci a Najeriya.

Ta ce, wasu daga cikin masu zuba jarin tuni suka fara gine-ginen masana’antu, wasu kuma suna shigo da kayayyakin aikin masana’antun.

Ministar masana’antun ta Najeriya ta alakanta yawan masu sha’awar zuba jarinsu a Najeriya bisa ziyarce-ziyarcen da shugaban kasa ke yi zuwa kasashen waje domin kwadaitar da ’yan kasuwar dake waje irin dimbin arzikin da Najeriya ke da su.

“Ina son na shaida maku cewa kamar yadda kuka sani ne ziyarar farko da shugaban kasa ya kai zuwa kasar Indiya ya sami nasarar kulla mu’amalar kasuwanci ta dala biliyan 14, baya ga haka kuma wani katafaren kamfanin sarrafa karafa na kasar ta Indiya ya bijiro da bukatar saka jarinsa a Najeriya na kudin da ya kai dala biliyan 7, kuma muna tattaunawa a kan wannan bukata tasa a kwamitin ministoci.”

Ta ce, ko a kwanan nan ma kamfanin Koka-Kola ya kara saka jarinsa na dala biliyan 1 na tsawon shekaru biyar, kari kuma a kan wanda ya saka a baya na dala biliyan 1.3 a shekaru 10 da suka gabata.

Haka kuma ministar ta sanar da cewa, ko a makon da ya gabata, Najeriya ta samu karin dala biliyan goma daga ’yan kasuwa masu saka jari a harkar mai da iskar gas, inda ta yi amfani da wannan dama wajen musanta zargin da ake cewa kamfanin mai na Shell ya janye jarinsa daga Najeriya.

“Ina tabbatar maku da cewa, kamfanin ba zai bar Najeriya ba, asali ma dai yana shirye-shiryen kara adadin jarinsa ne a Najeriya.” (Garba Abdullahi Bagwai)