logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin Jamus ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi

2024-02-18 20:43:30 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a jiya, yayin da yake halartar taron tsaro na Munich.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan Jamus wajen kara taka muhimmiyar rawa kan harkokin kasa da kasa da yankuna, kana tana fatan bunkasa fahimtar juna, da nuna goyon baya, da kara yin imani da juna, da yin hadin gwiwa a tsakaninta da Jamus, don ba da tabbaci ga dukkanin duniya baki daya.

A nasa bangare kuwa, Scholz cewa ya yi, tattalin arzikin Jamus yana shiga tsarin raya duniya na bai daya, kuma Jamus ta cimma moriya daga ciniki cikin ‘yanci. Kaza lika Jamus na adawa da ra’ayin ba da kariya ga cinikayya, da ra’ayin yanke hulda da sauran kasashe, tana kuma farin ciki da ganin Sin ta samu ci gaba, kana tana son samar da yanayin yin cinikayya mai kyau ga kamfanonin sauran kasashe dake Jamus.

Har ila yau a dai wannan rana, shugaban kasar Serbia Aleksandar Vučić ya gana da Wang Yi. A yayin ganawar da suka yi, Wang Yi ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Serbia yana da karfi, ya kuma dace da moriyar bangarorin biyu a dogon lokaci. Kuma Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Serbia, wajen tabbatar da ikon mulkin kai, da cikakken yankin kasa, da bin ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD, da kuma kiyaye adalci a duniya baki daya.

A yayin taron tsaron na Munich, Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Birtaniya, da wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro, da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, da Argentina, da Canada, da Poland, da Mongolia, da Ukraine da sauransu. (Zainab Zhang)