logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon murnar bude taron kolin AU

2024-02-17 20:33:23 CMG Hausa

Yau Asabar 17 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 37.

A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, kuma kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin da kasashen Afrirka na kara bunkasa, abun dake haifar da babban tasiri ga ci gaban duniya. Ya ce AU tana himmatuwa wajen hada kan kasashen Afirka, da kokarin dunkule duk nahiyar baki daya, tare da gina yankin cinikayya maras shinge.

Kasar Sin ta kuma taya AU murnar shiga cikin kungiyar G20, abun da a cewarta, zai kara wakilci, da karfin fada-a-ji na kasashen Afirka a harkokin dukkanin duniya.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, a shekarar da ta gabata, dangantakar Sin da Afirka ta bunkasa yadda ya kamata, kuma an yi nasarar gudanar da shawarwari tsakanin shugabannin Sin da na Afirka, inda suka kudiri aniyar goya wa juna baya wajen lalubo hanyoyin zamanantar da kansu, da kirkiro yanayi mai kyau ga cimma muradunsu.

A shekara ta 2024, za’a gudanar da taron FOCAC a sabon zagaye, wato taron dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, kuma shugaba Xi ya sha alwashin yin kokari tare da takwarorinsa na kasashen Afirka, wajen samar da alfanu ga al’ummunsu, da tsara sabuwar taswirar hadin-gwiwar Sin da Afirka, gami da kara gina al’ummu masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)