logo

HAUSA

An nada shugaba Tinubu a matsayin gwarzon kiwon lafiya na AU

2024-02-17 17:06:12 CMG Hausa

An nada shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, a matsayin gwarzon kungiyar tarayyar Afirka ta AU, na bunkasa fannonin kiwon lafiyar al’umma, bisa kwazonsa wajen aiwatar da hadin gwiwa da kirkire- kirkire, da mayar da hankali ga raya fannin.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Juma’a cikin wata sanarwa, kakakinsa Ajuri Ngelale, ya ce nadin shugaba Tinubu na zuwa ne sakamakon yadda gwamnatin Najeriya mai ci, ta yi nasarar horas da ma’aikatan lafiya dake kusa da al’umma har 120,000 cikin watanni 16, da shirin rubanya cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake dukkanin sassan Najeriya, daga 8,800 zuwa sama da 17,000 cikin shekaru 3 masu zuwa.

Ngelale ya ce nadin Tinubu a matsayin gwarzon bunkasa fannonin kiwon lafiyar al’umma, na kunshe ne cikin wata wasika da cibiyar kandagarki, da yaki da cututtuka ta Afirka ta mikawa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya.(Saminu Alhassan)