logo

HAUSA

Dennis Francis: Bikin Bazara kyauta ce da kasar Sin ta baiwa duniya

2024-02-17 17:09:14 CMG Hausa

Kwanan nan ne shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, Dennis Francis, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a Beijing.

A shekarar da muke ciki, an ayyana Bikin Bazara, wato bikin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin, a matsayin lokacin hutu na MDD a hukumance. Game da wannan batu, Mista Dennis Francis ya ce bikin tamkar kyauta ce da kasar Sin ta baiwa duk duniya, inda kuma ya mika gaisuwar barka da shiga sabuwar shekarar ga daukacin Sinawa.

A yayin ziyararsa kasar Sin wannan karo, Mista Francis ya kara fahimtar kwazon aiki na Sinawa, ta hanyoyi daban-daban, ciki har da shiga jirgin kasa mai saurin gudu, da yin tattaki zuwa yankunan karkara. Ya ce, sauye-sauyen da kasar Sin ta yi, sun samu babbar nasara, abun da ya samar mata da babban ci gaba a fannoni da dama, ciki har da inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kawar da talauci, da kiyaye hakkokin mata, da samar da ilimi da sauransu, wadanda su ne burikan da MDD ke kokarin neman cimmawa a fannin samar da dauwamammen ci gaba.

Jami’in ya kuma kara yin kira da a tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da jaddada cewa, al’ummar wurin na matukar bukatar agajin jin-kai. Ya kuma sake nanata cewa, in dai babu zaman lafiya, ba za a samu ci gaba mai dorewa ba. (Murtala Zhang)