logo

HAUSA

‘Yan sandan tekun kasar Sin sun kori jirgin ruwan kasar Philippines da ya yi kutse cikin yankin ruwan tekun dake kewaye da tsibirin Huangyan

2024-02-16 16:35:39 CMG Hausa

Mai magana da yawun hukumar tsaron tekun kasar Sin Gan Yu ya bayyana cewa, jiya Alhamis ranar 15 ga wata, jirgin ruwa mai lamba 3005 mallakin hukumar kula da albarkatun ruwa ta kasar Philippines ya kutsa kai cikin yankin ruwan tekun dake kewaye da tsibirin Huangyan mallakin kasar Sin. Jirgin ruwan ya yi biris da gargadin da ‘yan sandan tsaron tekun kasar Sin suka yi masa sau da dama, al’amarin da ya sa ‘yan sandan suka dauki matakan da suka dace na korar sa daga wurin.

Babu tantama, kasar Sin na da ikon mallakar tsibirin Huangyan gami da yankin ruwan tekun dake kewaye da shi. ‘Yan sandan tsaron tekun kasar Sin sun dauki matakan ne domin kiyaye halastaccen hakkin kasar a yankin tekun nata, tare da kiyaye cikakken ‘yancin kasa gami da hakkokinta a yankunan teku. (Murtala Zhang)