logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa don tinkarar barazanar ta’addanci

2024-02-16 16:49:40 CMG Hausa

A wajen taron yaki da ta’addanci da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a jiya Alhamis 15 ga wata, wakilin dindindin na kasar Sin dake majalisar, Zhang Jun ya jaddada muhimmancin karfafa hadin-gwiwa domin yakar barazanar ta’addanci, inda kuma ya yi kira da a murkushe duk wani nau’in ta’addanci, da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Jami’in ya ce, ta’azzarar rikicin Palesdinu da Isra’ila ya janyo karin munanan laifuffukan nuna kiyayya da aka aikata a kasashe daban-daban, kuma ana kara fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci. Abun dake gaban komai a halin yanzu shi ne, tsagaita bude wuta a zirin Gaza, don kar halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya ya ci gaba da tabarbarewa.

Jami’in ya kuma ce, yankin yammacin Afirka da na Sahel na fuskantar babbar barazanar hare-haren ta’addanci, kuma babban dalilin da ya sa haka shi ne rashin kwarewa wajen murkushe su. Don haka ya zama dole MDD da sauran kasashen duniya su yi la’akari da bukatun kasashen Afirka, da kara ba su taimako.

Ha wa yau, jami’in ya ce, har kullum kasar Sin tana maida hankali sosai wajen halartar hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da ta’addanci. Kwanan nan ne kasar ta bullo da takardar bayani kan tsarin doka da matakan yaki da ta’addanci, inda aka takaita muhimman ayyuka gami da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin yakar ta’addanci. Kuma a nan gaba, Sin za ta ci gaba da inganta hadin-gwiwa tare da sauran kasashe, domin aiwatar da shawarar kiyaye tsaro a duniya da shugaban kasar ya bullo da ita. (Murtala Zhang)