logo

HAUSA

Adadin Zirga-zirgar Fasinjoji A Jiragen Kasa Ya Zarce Miliyan 230 A Rabin Farko Na Wa’adin Hutun Bikin Bazara

2024-02-15 20:13:13 CMG Hausa

Kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin, ya ce adadin zirga-zirgar fasinjoji a jiragen kasa a rabin farko na wa’adin kwanaki 40 da ake kwashewa ana gudanar da shagulgulan murnar bikin Bazara a kasar ya zarce miliyan 230.

Kamfanin ya ce, a jiya Laraba, adadin fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta jiragen kasa a Sin ya kai miliyan 14.25, wanda hakan ya kafa wani sabon tarihi, a yawan adadin fasinjoji da suka yi zirga-zirga a rana guda, yayin tafiye-tafiye mafiya yawa da ake yi a lokacin na murnar bikin Bazara.

Har ila yau, kamfanin ya yi hasashen cewa, a yau Alhamis, adadin na iya kaiwa miliyan 15.2, yayin da kwanaki 8 na hutun za su kammala a ranar Asabar.

Bikin Bazara a bana ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairu, shi ne kuma bikin gargajiya mafi girma da ake gudanarwa a kasar Sin. A bana an fara samun yawaitar tafiye-tafiye domin bikin tun daga ranar 26 ga watan Janairu, ana kuma fatan kammalar hakan a ranar 5 ga watan Maris.  (Saminu Alhassan)