logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya kaddamar da katafaren filin wasannin motsa jiki gabanin gasar wasanni ta nahiyar Afirka

2024-02-14 16:12:47 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya kaddamar da katafaren filin wasannin motsa jiki na Borteyman, gabanin gasar wasannin nahiyar Afirka karo na 13 da Ghana za ta karbi bakunci a wata mai zuwa.

Cikin jawabinsa na kaddamar da filin wasan a jiya Talata, shugaba Akufo-Addo, ya ce kasarsa ta yi namijin kokari tun daga shekarar 2021 zuwa wannan lokaci, wajen ganin an kammala gina filin wasan, wanda ka iya daukar ‘yan wasa a kalla 5,000, da jami’ai 3,000, da dubban ‘yan kallo wadanda za su ziyarci gasar domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Bisa kiyasi, gasar da za ta gudana a wata mai zuwa, za ta ja hankalin masu bibiyarta da yawansu ya kai biliyan 2.2, ta kafofin da aka saba da su, da ma sabbin kafofin sada zumunta na yanar gizo.

Katafaren filin wasan na Borteyman dake birnin Accra, na kunshe da sassan gudanar da wasan linkaya, da kwallon tennis, da handball, da volleyball.

Mashirya gasar a Ghana, sun ce ya zuwa ranar Talata, kasashen Afirka 49 sun riga sun bayyana aniyarsu ta shiga a dama da su a wasannin gasar. (Saminu Alhassan)