logo

HAUSA

Shin Tattalin arzikin Sin zai Ruguje? Jita-jita ne kawai

2024-02-14 08:01:26 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, aka fitar da alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar Sin, wanda ke nuna karuwar yawan hajoji da kayayyakin masarufi da Sin ta sayar, zuwa kashi 4.6 cikin 100 kan na shekarar 2022, wanda ya karu da sama da kashi 2 cikin 100. Wannan na kara tabbatar da cewa, alkalumann tattalin arzikin kasar Sin sun inganta, kuma cinikayyar hajojin kasar ta zarce yadda ake zato. 

Sanin kowa ne cewa, baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma damarmaki na yin kasuwanci da baki daga waje ke sha'awa matuka. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya yake fuskantar tafiyar hawainiya, kuma sakamakon durkushewar manufofi a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ya fito fili. 

Amma abin farin ciki shi ne, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba, ya kuma ci gaba da farfadowa, kuma yana ci gaba da zama muhimmin injin na ci gaban tattalin arzikin duniya. Lamarin dake kara baiwa ’yan kasuwa daga sassan duniya karfin gwiwa da sha’awar kara shiga babbar kasuwar kasar don gudanar da kasuwanci da samun babbar riba.

A bangaren masana'antun kasa da kasa kuwa, wani abu mai matukar muhimmanci shi ne, kyakkyawan fata a lokacin da kasuwar duniya ke fama da rashin tabbas. Yayin da wasu makiya ci gaban kasar Sin ke yada bayanai marasa tushe game da tattalin arzikin kasar, wai zai ruguje. Sai dai bankin duniya ya yi hasashen cewa, a bana tattalin arzikin Sin zai bunkasa da kaso 5.6 cikin 100, yayin da OECD kuma ya yi hasashen bunkasar za ta kai kaso 5.4, kana asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen bunkasar zuwa kaso 5.2 cikin100.

Masu fashin baki na cewa, kwanciyar hankali da dorewar manufofin tattalin arzikin kasar Sin, sun karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa wajen kara neman shiga babbar kasuwar kasar. Sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashe a duniya dake samar da damammakin ci gaba ga kamfanonin kasa da kasa. (Muhammed Yahaya, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)