logo

HAUSA

Masana’antar Kera Jiragen Ruwa Ta Sin Ta Samu Karin Riba A Shekarar Bara

2024-02-14 16:01:23 CMG Hausa

Alkaluma daga kungiyar kamfanonin kera jiragen ruwa ta kasar Sin, sun nuna yadda masana’antar ta samu karin riba a shekarar 2023 da ta gabata, ciki har da riba, da kudin shiga, da karin damar gogayya da takwarorinsu na sassan duniya.

Alkaluman sun nuna karuwar ribar kamfanonin kera jiragen ruwan na Sin da kaso 131.7 bisa dari a shekara, inda ribar ta kai kudin Sin yuan biliyan 25.9, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.64. Kaza lika yawan kudin shigarsu ya kai yuan biliyan 623.7, wanda hakan ya shaida karuwar kaso 20 bisa dari a shekara.

A dai shekarar ta 2023, kamfanonin kera jiragen ruwa na kasar Sin, sun gaggauta bunkasa fasahohinsu na dijital, da ingiza kirkire-kirkiren fasahohi. Har ila yau, kamfanoni da dama na Sin dake aiki a wannan fanni, sun shiga jerin 10 na farko a duniya ta fuskar fitar da hajojinsu, da karbar sabbin oda, da odar gaggawa daga mabukata. Bugu da kari, masana’antar kera jiragen ruwa ta Sin na kan gaba a duniya, idan aka yi la’akari da dukkanin alkaluman bunkasar ayyukan sashen.

Game da hakan, sakataren kungiyar kamfanonin kera jiragen ruwa ta kasar Sin Li Yanqing, ya ce kamfanonin Sin za su wuce gaba, tare da kyautata ci gaba mai inganci, da takara mai nagarta. (Saminu Alhassan)