logo

HAUSA

Majalisar dokokin Najeriya za ta kafa doka kan albarkatun ma'adinai da ba a hako ba

2024-02-13 15:48:48 CMG Hausa

 

Rahotanni daga Najeriya na cewa, majalisar dokokin kasar na duba yiwuwar samar da wata cikakkiyar doka, da za ta mayar da hankali kan magance matsalolin da suka shafi albarkatun ma’adinai da ba a hako su ba, a wani mataki na cin gajiyar dimbin arzikin ma’adinan da Allah ya horewa kasar da ma bunkasa tattalin arzikinta

Da yake jawabi a yayin wani taron tsara manufofi da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar, mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar, Benjamin Kalu, ya yi karin haske kan dokar da ake fatan kafawa, inda ya ce, manufar dokar da aka gabatar ita ce, samar da ingantaccen tsarin gudanar da bincike, da hakowa, da cin gajiyar albarkatu masu muhimmanci.

Ya ce, an gabatar da dokar ce a matsayin daftarin doka: Dokar ma'adinai ta Najeriya da aka yi wa gyara, yana mai jaddada cewa, ba a cin gajiyar dimbin albarkatun ma'adinan kasar saboda dogaro da kudaden shigar danyen mai.

Ya bayyana cewa, duk da yawan ma'adinai masu amfani na kasuwanci da kasar ke da su, sashin sarrafa ma'adinai na kasar, yana ba da gudummawar kalilan na GDP, yana mai bayyana burin gwamnati na bayar da gudummawar kashi 3 cikin 100 ga GDPn kasar nan da shekarar 2025.(Ibrahim)