logo

HAUSA

Sin Ta Fadada Tsarin Sadarwa A Shekarar 2023

2024-02-12 16:31:42 CMG Hausa

Ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shekarar 2023, Sin ta ci gaba da fadada hanyoyin sadarwar kasar.

Ma’aikatar ta ce, a shekarar da ta gabata, Sin ta yi nasarar shimfida wayoyin sadarwa na tsawon kusan kilomita miliyan 4.74, wanda ya kawo adadin zuwa kilomita miliyan 64.32 na wayoyin sadarwar kasar.

Bayanai na nuna cewa, kasar Sin tana da kusan tashoshin sadarwa na intanet biliyan 1.14 a karshen shekarar da ta gabata, fiye da miliyan 64.86 kan na shekarar 2022.

A wata takardar bayani da aka fitar a watan da ya gabata, ma'aikatar ta sanar da cewa, kasar Sin na shirin tsawaita fasahar sadarwar wayar salula ta 5G da tsarin wayoyin sadarwa mai saurin Mbps dubu 1 zuwa dukkan gundumomi da garuruwan da ke kan iyakokin kasar nan da karshen shekarar 2025.(Ibrahim)