logo

HAUSA

Bangaren Samar Da Kaya Ko Aiwatar Da Ayyukan Hidima Da Ma’aikatan Kamfani Ke Yi Ya Fadada A Kasar Sin A Shekarar 2023

2024-02-12 20:35:19 CMG Hausa

Alkaluma daga ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin sun bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, bangaren samar da kaya ko aiwatar da ayyukan hidima da ma'aikatan kamfani ke yi, ya samu ci gaba matuka a kasar a shekarar da ta gabata.

A cewar bayanai, kamfanonin kasar Sin sun kulla kwangiloli masu ruwa da tsaki da darajarsu ta kai kudin Sin RMB kusan yuan tiriliyan 2.87, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 404 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 17.6 bisa dari na shekarar 2022.

Darajar kwangilolin da aka aiwatar, ta kai kusan yuan tiriliyan 1.96, wanda ya karu da kashi 18.6 kan na shekarar 2022.

Daga cikin wannan adadi, darajar kwangilolin da aka daddale tsakanin kamfanonin kasar Sin da na ketare, ya karu da kashi 12.9 bisa na shekarar 2022, wanda ya kai kusan yuan tiriliyan 1.49. (Ibrahim)