logo

HAUSA

Najeriya ta amince da bukatar kafa hukumar hadin gwiwa tsakanin ta da jamhuriyar Benin

2024-02-12 15:56:56 CMG Hausa

Ministan lura da harkokin kasashen waje na tarayyar Najeriya Yusuf Tuggar ya tabbatar da amincewar gwamnatin kasar game da bukatar da aka gabatar ta neman kafa hukumar din-din-din ta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin.

Ya tabbatar da hakan ne a Abuja a karshen makon jiya lokacin da yake karbar bakuncin wata kungiya mai rajin tabbatar da ganin kasashen biyu sun amince da samar da wannan hukuma da za ta rinka kula da harkokin cigaban kasashen ta fuskar tsaro da kasuwanci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministan ya bayyana cewa da jimawa aka samar da wannan hukuma tun a shekara ta 2014, to amma saboda rashin motsinta yadda ya kamata ya sanya ake ganin kamar ma babu ita, a don haka yanzu akwai bukatar a sake farfado da ayyukanta.

Ya ce wanzuwar hukuma na da mahimmancin gaske saboda ta kunshi bangarorin ‘yan kasuwa da na gwamnati da kungiyoyin masu zaman kansu wadanda dukkansu suna da ruwa da tsaki a kan harkokin dake wakana a kan iyakokin kasashen biyu.

“Batun sha’anin karuwar tabarbarewar tsaro yana da nasaba da karancin lura da yanayin zamantakewar rayuwar mutanen da suke zaune a kan iyakoki, saboda a irin wadannan yankuna ne ‘yan ta’adda suka fi fakewa suna kulle kullen suna ta’addanci.”

Da yake jawabi, shugaban gudanarwar kungiyar Ambasador Oguntuase Kayedo ya ce samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin zai taimaka mutuka wajen gina al’umma tare da dorewar kasuwancin al’umomin kasashen biyu, inda ya ce nuna bukatar samar da ita wannan hukuma ya samo asali ne daga wanzuwar makamanciyarta tsakanin Najeriya da sauran kasashen makwabta musamman jamhuriyar Nijar.

“Mun yarda cewa a kowanne matsayi ko mataki mutane su kan kafa kungiyoyi, imma dai na ‘yan kasuwa ko addini ko kuma kungiyoyin al’adun garjiya.” (Garba Abdullahi Bagwai)