logo

HAUSA

Firaministan kasar Nijar ya gana da tawagar ‘yan Nijar dake zaune a kasar Benin

2024-02-11 16:14:25 CMG Hausa

A jiya Asabar 10 ga watan Fabrairun shekarar 2024, firaministan jamhuriyar Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da mambobin Diaspora na ‘yan Nijar dake kasar Benin, a karkashin jagorancin shugaban babban zauran shawara na ‘yan Nijar da ke zaune a Benin, Issa Boubacar Alpha a fadar firaminista da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Ita dai wannan tawaga ta zo a Yamai ne cikin tsarin tattara gudummawar ‘yan Nijar game da asusun zumunci domin ceton kasa na FSSP.

Bayan ganawaru tare da Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine, shugaban tawagar Issa Boubacar Alpha ya shaida wa manema labarai cewa, sun yi amfani da wannan dama domin jinjinawa sabbin hukumomin kasar Nijar, haka kuma da tabbatar masa cewa suna rayuwa ba tare da wata matsala ba tare da al’ummar Benin, dukkan al’umomin kasashen biyu na rayuwa tare cikin armashi da kwanciyar hankali.

Bangarorin biyu sun tattauna kan dandalin da suke jira na ‘yan Nijar da ke kasashen waje, inda za’a samu zarafin tattauna dukkan matsalolin ‘yan Nijar da ke zaune a kasashen waje, in ji shugaban babban zauren shawara na ‘yan Nijar da ke ketare.

A nasa bangare, Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine, ya nuna farin cikinsa ga mutanen Diaspora bisa ga halayyarsu mai kyau ta zaman rayuwa a kasar da ta karbi bakuncinsu, kafin kuma ya ba da kwarin gwiwa ga ‘yan Diaspora na su kara azama wajen kishin kasa da karfafa zumunci ko wace rana, tare da girmama dokokin kasar Benin da ta karbi bakuncinsu.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.