logo

HAUSA

Kasar Sin: Ana Sa Ran Masu Yawon Bude Ido Za Su Yi Tafiye-tafiye Sama Da Biliyan 6 A Shekarar 2024

2024-02-11 15:50:40 CMG Hausa

Hukumar kula da yawon bude ido ta kasar Sin ta ce, ana sa ran masu yawon bude ido na kasar Sin za su tafiye-tafiye sama da biliyan 6 a cikin gida a bana, kuma jimilar tafiye-tafiyen da masu yawon bude ido da za su shigo kasar Sin da wadanda za su fita wajen kasar za su yi, za ta zarce miliyan 260.

Rahoton da hukumar ta fitar, wanda ya hada da nazarin yanayin bangaren yawon bude ido na kasar Sin a shekarar 2023 da hasashen shekarar 2024, ya bayyana yadda bangaren ya farfado sosai a bara.

A cewar rahoton, a shekarar 2023, yawon bude ido a kasar Sin ya karu da kaso 100 bisa 100 ta fuskar adadin masu yawon bude ido da ma kudin shigar da bangaren ya samu, inda ya farfado da sama da kaso 80 a matakin da yake a shekarar 2019.

Haka kuma adadin wadanda suka shigo kasar Sin da wadanda suka fita daga kasar domin yawon bude ido shi ma ya karu, inda ya zarce miliyan 190, karuwar kaso 280 a kan na shekarar 2022.

Ayarin masu bincike na hukumar ya kara da bayyana cewa, sha’awar bulaguro a tsakanin mazaunan kasar Sin ya kasance kan wani babban matsayi a duk tsawon shekarar 2023, inda kuma mutanen suka bayyana gamsuwarsu matuka. (Fa’iza Mustapha)