logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Gaggauta Gina Tsarin Juya Shara

2024-02-10 16:11:50 CMG Hausa

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da wani daftarin ka’idoji da ya fayyace burika da matakan gaggauta samar da wani tsarin juya bola da zai karfafa tubalin kare muhalli da rage hayakin Carbon, domin kasar ta kai ga samun ci gaba mai inganci.

Daftarin ya jaddada bukatar kiyaye manufar tattalin arziki da ta shafi samar da kayayyaki ta hanyar sake amfani da albarkatu, wadda ta shafi batutuwa 3, wato rage barna da sake amfani da kayayyaki da juya shara, da zummar kara ingancin amfani da albarkatu ta hanyar bayar da kulawa sosai da juya kayayyaki da bola yadda ya kamata.

Zuwa shekarar 2025, za a kafa tsarin juya bola da ya shafi dukkan bangarori, inda yawan bolar da ba ta ruwa ba kamar ta ma’adinai da toka da gwal, da za a yi amfani da ita zai kai ton biliyan 4, kana jimilar irin wannan bola da za a juya za ta kai kaso 60 cikin 100.

A yanzu haka, yawan albarkatun da ake iya sabuntawa, wanda ake amfani da su, kamar ragowar baki da jan karafe da goran ruwa, ya kai ton miliyan 450 a shekara.

Daftarin ya kuma bayyana bukatar samar da masana’antar juya bola, wadda za ta mamaye dukkan bangarorin samar da kayayyaki da na rayuwa, tare da cimma burin samar da yuan triliyan 5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 703.87 a ko wace shekara, ya zuwa shekarar 2025. (Fa’iza Mustapha)