logo

HAUSA

Yawan Masu Kallon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2024 Da CMG Ya Shirya Ya Karya Matsayin Bajimta

2024-02-10 16:30:55 CMG Hausa

A ranar 9 ga wannan wata da karfe 8 na dare, aka gabatar da shagalin murnar Bikin Bazara na shekarar 2024 da CMG ya shirya kamar yadda aka tsara. Shagalin ya kunshi shirye-shirye da nau'ikan gabatarwa da fasahohi, domin nuna abubuwa da al’adun dake wakiltar duk kasar Sin. Ya zuwa karfe 2 na dare a yau Asabar 10 ga wata, yawan masu kallon shagalin a wannan karo ya kai biliyan 14 da miliyan 200, wanda ya karu da kashi 29 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara. Har ila yau, ya karya matsayin bajimta a fannonin da suka shafi yadawa da kallon shagalin da sauransu.

Yawan masu kallon shagalin kai tsaye a wannan karo ya kai matsayin koli. Ya zuwa karfe 8 na safe a ranar 10 ga wannan wata, yawan masu kallon shagalin kai tsaye ya kai miliyan 795, kuma an kalli shagalin sau fiye da biliyan 1 da miliyan 689, wanda ya karu da kashi 15.13 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.

Hakazalika, yawan kafofin watsa labaru na kasashen waje da suka yada shagalin a wannan karo ya karya matsayin bajimta. Tashoshin harsunan Ingilishi da Spananci, da Faransanci, da Larabci, da Rashanci na gidan telebijin na kasa da kasa na kasar Sin wato CGTN, da dandalolin watsa labaru na harsuna 68, da kuma kafofin watsa labaru fiye da 2100 daga kasashe da yankuna 200 ciki har da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Italiya, da Rasha, da Japan, da Brazil, da Australia, da Indiya, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Singapore, da Afirka ta Kudu da sauransu, sun gabatar da shagalin a wannan karo kai tsaye tare da bayar da labarai, ya zuwa karfe 12 na dare a ranar 9 ga wannan wata, yawan masu kallo ta kafofin a duk duniya ya zarce miliyan 649, kana an kalli shagalin sau miliyan 210. (Zainab Zhang)