logo

HAUSA

Yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ranar 8 ga wata ya kai miliyan 12.446 a kasar Sin

2024-02-09 10:17:26 CMG Hausa

Sakamakon yawan zirga-zirgar da Sinawa suke yi a lokacin bikin bazarar kasar, yawan fasinjojin da jiragen kasan kasar suka dauka jiya Alhamis, ya kai miliyan 12.446. Kana yau Jumma’a jajibiri ne na bikin bazara, wato sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, inda Sinawa suka fara bukukuwan murnar bikin, don haka, zirga-zirgar mutane ta jiragen kasa ta ragu, inda ake sa ran samun jigilar fasinjoji miliyan 8.3 da jirgin kasa.

Duk da haka, a yau din, an tsara samar da karin jiragen kasa guda 979 don kwashe fasinjoji, ta yadda ake iya biyan butakar dake akwai.(Safiyah Ma)