logo

HAUSA

Kungiyar Ecowas za ta bi matakan diplomasiyya game da ficewar wasu kasashe daga cikinta

2024-02-09 09:09:27 CMG Hausa

A jiya Alhamis 8 ga wata, kungiyar Ecowas ta kammala taronta na gaggawa na ministocin kasashen waje, inda ta tattauna a kan matakin da wasu kasashe membobinta guda uku suka dauka na ficewa daga cikin kungiyar.

A yayin taron da suka gudanar a birnin Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya, taron ministocin ya bayyana takaici a game da halayyar gwamnatocin sojin kasashen Senegal, Burkina Faso da kuma Niger wajen aikata manufofin kungiyarta Ecowas a ko da yaushe.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar shi ne ministan harkokin kasashen waje na tarayyar Najeriya ya yi wa manema labarai karin bayani a game da abubuwan da taron nasu ya cimma.

“Ita Ecowas muhimmancinta talikan da suke ciki ba wai gwamnatocin ba, saboda haka muna kara jaddada kokari da za mu ci gaba da yi ta hanyar diplomasiyya na shawo kan su domin su zauna gidanmu daya su ’yan uwa ne kuma zaman lafiya ake nema a wannan yankin namu, kusan wannan fita sai a ce ma mai yiwa wahalar da zai jawowa talaka ya mafi takunkumin da ake maganar na saka.”

To ko taron ya tabo batun yiwuwar cirewa janhuriyyar ta Nijar takunkumi?

“Eh to wannan dama ai ko da yaushe duk cikin tattaunawar da muke yi muna jaddada zancen cire takunkumi, kuma so ake yi, su ma su duba, su ga inda wasu abubuwa da ya kamata su yi domin a sami rangwame da kuma saukin cimma matsaya daya, su ma su yi ta bangaren su.”

A kan halin da kasar Senegal ke ciki kuwa bayan dage babban zaban kasar da aka yi, ministan harkokin wajen na Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce, “Ita Senegal an tattauna amma ba a saka shi cikin rahoto ba saboda akwai ka’idar Ecowas, lokacin da aka tura takardar gayyatar wannan taro, batun dage zabe na Senegal bai riga ya faru ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)