logo

HAUSA

An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin

2024-02-08 10:44:58 CGTN HAUSA

A jiya Laraba, aka kammala aikin bitar liyafar bikin murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin karo na 5, da CMG ta shirya. Kide-kide da wake-wake da raye-raye da kuma shirye-shiryen wasan kwaikwayo da Kongfu da sauransu, za a gabatar da wadannan shirye-shirye masu kayatarwa a babban dandali dake birnin Beijing da dai sauran kananan dandaloli 4 a wurare daban-daban. Ya zuwa yanzu, CMG ta kintsa tsaf kan wannan biki, ana maraba da Sinawa dake bazuwa a duk fadin duniya domin shakatawa da wannan gaggarumin biki mai kunshe da fasaha na zamani.

Allunan talabijin fiye da 3000 daga birane 90 na kasashe 49 za su watsa bidiyon wannan shagali kai tsaye, don a more farin ciki da kuma fatan alherin bikin bazara na kasar Sin. (Amina Xu)