logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya taya Ilham Aliyev murnar sake cin zaben shugabancin kasar Azerbaijan

2024-02-08 16:37:45 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga Ilham Aliyev, na sake cin zaben shugabancin kasar Azerbaijan, da samun damar sabunta wa’adin aikinsa a matsayin shugaban kasar.

Shugaba Xi ya mika sakon ne a yau Alhamis, inda ya ce yana dora muhimmanci kan aikin karfafa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Azerbaijan, kuma a shirye yake ya kokarta tare da shugaba Aliyev don kyautata huldar bangarorin 2 da inganta hadin gwiwar da suke yi zuwa wani sabon matsayi. (Bello Wang)