logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Portugal sun taya junansu murnar cika shekaru 45 da kulla hulda a tsakanin kasashen 2

2024-02-08 16:39:28 CMG Hausa

A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Portugal Marcelo de Sousa sun tura ma junansu sakonnin taya murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen 2.

Cikin sakonsa, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, yana daukar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Portugal da muhimmancin gaske, kuma a shirye yake ya kokarta tare da shugaba de Sousa, don zurfafa abokantakar dake tsakanin kasashen 2, wadda ta shafi dukkan fannoni daban daban. Ta yadda jama’ar kasashen 2 za su amfana, da ciyar da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Turai zuwa gaba, da samar da gudunmawa ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya, da zaman karko, da walwala a duk fadin duniya.

A nashi bangaren, shugaba de Sousa ya ce, kasar Portugal na son yin kokari tare da kasar Sin, don karfafa zumunta, da kara inganta huldar dake tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)