logo

HAUSA

A ko da yaushe kasar Sin na himmatuwa wajen inganta bude kofa ga kasashen waje da fadada mu'amalar jami'ai a tsakanin ta da kasashen ketare

2024-02-07 19:48:36 CMG Hausa

Kwanan nan, domin saukakawa baki 'yan kasashen waje neman lambobin wayar salula yayin shiga kasar Sin, wasu kamfanonin sadarwa, ciki har da China Telecom, China Mobile, China Unicom da sauran su sun kara samar da sassan bayar da hidima guda 9 a filayen jiragen sama na biranen Beijing, Shanghai, Guangzhou, Kunming, Chengdu, Xiamen da sauransu, kana sun kara sabbin wuraren ba da hidima guda shida a wasu muhimman wurare masu yawan mu'amala da kasashen waje, kamar su biranen Beijing, Guangzhou, Shenzhen, Xi'an, da kuma Qingdao da dai sauransu.

A yayin da yake ba da amsa game da wannan batu a gun taron manema labaru da aka saba yi na yau Laraba 7 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya nuna cewa, yayin da kasar Sin ke ci gaba da inganta matakan da take dauka don saukaka musayar jama'a a tsakanin ta da kasashen ketare, 'yan kasar Sin na iya fita waje cikin kwanciyar hankali a saukake, kana abokai na kasashen waje da ke zuwa kasar Sin su ma sun samu sauki.

An kuma bayar da labarin cewa, a ranar yau din, kamfanin 360 ya fitar da rahotanni biyu, da ke fallasa yadda Amurka ke kawo illa ga tsaron yanar gizo ta Intanet. Game da haka, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, ana iya daukar Amurka a matsayin "tushen duk wani sharri" na kalubalen dake tattare da hadarin yanar gizo, kuma babu wata kasa da za ta tsira daga barazanar hare-haren na Amurka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)