logo

HAUSA

Shugabannin Sin sun mika gaisuwar sabuwar shekara ga tsoffin shugabannin kasar

2024-02-07 20:04:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar, sun ziyarta ko sun ba jami’an sassa masu ruwa da tsaki umarnin ziyartar tsoffin shugabannin kasar domin mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar kasar dake karatowa.

Shugaba Xi da sauran shugabannin kasar sun yi wa tsoffin shugabannin fatan koshin lafiya da tsawon rai tare da gudanar da bikin cikin farin ciki.

A nasu bangaren tsoffin shugabannin sun jinjinawa ci gaba mai kwari da jam’iyyar kwaminis ta kasar da rundunar sojin kasar da ma al’ummar kabilu daban daban suka samu wajen gina kasar zuwa ta zamani mai bin tsarin gurguzu ta kowacce fuska, karkashin kwamitin kolin JKS da shugabancin Xi Jinping.

Sun kuma yi kira da a yi kokari cikin kwarin gwiwa, a yunkuruin gina kasa mai karfi da karin kuzari ta kowane bangare ta hanyar zamanintar da kasar. (Fa’iza Mustapha)