logo

HAUSA

Xi ya mika sakon gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ga wadanda ba ‘yan JKS ba

2024-02-07 20:59:20 CMG Hausa

Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS), ya mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, ga jam’iyyun da ba na JKS ba da kungiyar masu masana’atu da ‘yan kasuwa da daidaikun mutane marasa jam’iyya, gabanin shiga sabuwar shekarar.

Xi Jinping wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar kolin rundunar sojin kasar, ya mika gaisuwar ce a lokacin da ya halarci taron shekara-shekara na mambobin da ba na JKS ba da ya gudana yau Laraba a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.