logo

HAUSA

Kasar Sin ta taya Nangolo Mbumba murnar zama sabon shugaban Namibia

2024-02-06 19:57:52 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta taya Nangolo Mbumba murnar zama shugaban kasar Namibia.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai na yau Talata, inda ya ce ya yi ammana karkashin shugabancin Nangolo Mbumba, Namibia za ta ci gaba da rike kuzarin na neman ci gaba da cimma sabbin nasarori a tafarkin raya kanta.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na daukar dangantakarta da Namibia da matukar muhimmanci, kuma a shirye take ta hada hannu da ita wajen zurfafa musaya da hadin gwiwa a bangarori daban daban da daukaka muhimmiyar dangantakar hadin gwiwa dake tsakaninta da Namibia zuwa sabon mataki. (Fa’iza Mustapha)