logo

HAUSA

Ana gudanar da harkokin kasuwancin yadda ya kamata gabanin bikin bazara na kasar Sin

2024-02-06 11:00:33 CMG Hausa

Yau Talata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan harkokin kasuwanci Sheng Qiuping ya bayyana cewa, bayanai kan harkokin kasuwanci na nuna cewa, ana gudanar da harkokin kasuwanci a sassan kasar Sin cikin tsari gabanin bikin bazara, musamman ma a fannoni guda uku.

Na farko shi ne, an samar da isassun kayayyakin da ake bukata. Akwai isassun amfanin gona da abinci kamar hatsi da man girki da madara da kayan lambu da nama da sauran kayayyakin yau da kullum da jama’a suke bukata a cikin kasuwannin sassan kasar Sin.

Na biyu shi ne, farashin kayayyakin bai canja ba. A ranar 4 ga wata, farashin hatsi da man girki da naman sa da na rago a manyan kasuwannin kasar, dai-dai yake da na farkon watan nan da muke ciki.

Na uku kuma, ana sayar da kayayyaki da yawa. A karshen watan Janairu, jimillar kayayyakin da kamfanonin kiri, wadanda ma’aikatar kasuwanci ta fi sanya ido, cinikayyarsu ta karu da kaso 19.9 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Disamba na shekarar 2023. A watan Janairu kuma, jimillar kayayyakin yau da kullum da aka sayar ta yanar gizo, ta karu da kaso 20 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)