logo

HAUSA

Firaministan Sin ya bukaci a kara himma wajen yaki da cin hanci da rashawa a aikin gwamnati

2024-02-06 10:11:50 CGTN HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bukaci a zage damtse, wajen ganin an aiwatar da manufofin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta cikakken tsarin mulkin kai, kana ya yi kira da a kara kaimi wajen kyautata halaye da mutuncin jam'iyyar, gami da yaki cin hanci da rashawa a cikin gwamnati.

Li, mamban zaunannen kwamitin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana haka ne a yayin taron majalisar gudanarwar kasar da aka shirya kan tafiyar da tsarin shugabanci mai tsafta.

Da yake jawabi a wurin taron, Li ya kuma yi na’am da ci gaban da gwamnatoci a dukkan matakai da sassansu suka samu a cikin shekarar da ta gabata, wajen inganta ayyukan jam'iyya, da tabbatar da gaskiya da yaki da matsalar cin hanci da rashawa. (Ibrahim Yaya)