logo

HAUSA

Yawan zirga-zirgar fasinjojin jiragen kasa a kasar Sin zai kai miliyan 12 da dubu 900 a ranar 6 ga watan

2024-02-06 10:58:07 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Sin na nuna cewa, yawan zirga-zirgar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye ta jiragen kasa a kasar Sin a jiya, ya kai miliyan 12 da dubu 198. Kana a yau 6 ga wata, ana hasashen adadin zai karu, inda ake zaton zai kai miliyan 12 da dubu 900, wannan ya sa aka kara samar da jiragen kasa 1789. A halin yanzu, zirga-zirga ta jiragen kasa a dukkan kasar Sin na gudana yadda ya kamata, kuma harkokin zirga-zirgar jiragen kasa na komawa kamar yadda aka saba a tashoshin jiragen kasa da matsalar yanayi ta shafa.

Lokacin bulaguro na bikin bazara na kasar Sin na bana yana daukar kwanaki 40 daga ranar 26 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Maris. Hukumomin zirga-zirga da sufuri na kasar Sin sun yi hasashen cewa, mutane kimanin biliyan 9 ne za su yi zirga-zirga tsakanin yankuna a fadin kasar a cikin wannan lokaci, wanda ya kusan ninka adadin a shekarar 2023. (Zainab)