logo

HAUSA

Sin na son shiga cikin kokarin da duniya ke yi kan ka'idojin tafiyar da fasahar AI

2024-02-06 10:12:36 CGTN HAUSA

 

Mataimakin ministan ilimi na kasar Sin, kana wakilin kasar a taron MDD kan tafiyar da dokokin fasahar AI Wang Jiayi ya bayyana cewa, kasarsa na son shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na inganta ka’idoji da yadda ake tafiyar da ayyukan da suka shafi fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam wato AI a takaice, ta yadda zai amfanar da dukkan bil-adama.

Wang Jiayi ya bayyana haka ne a gun taron koli na duniya karo na biyu, kan ka'idojin fasahar AI, taron yini biyu da hukumar kula da ilimi da kimiya da al'adu ta MDD UNESCO ta dauki nauyin shiryawa a birnin Kranj na kasar Slovenia.

Wang ya ce, tsare-tsaren tafiyar da harkokin fasahar AI da kasashe daban-daban suka gabatar, na nuna kwarewarsu ta hanyar da ta dace, kuma za ta iya samar da wani tushe na tattara ra'ayin kasashen duniya, da fito da tsare-tsaren gudanar da harkokin duniya tare.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana son sauraren dukkan bangarori, da gudanar da tattauna, da mu'amala, da yin hadin gwiwa kan fasahar AI na duniya, tare da gina budadden tsari, mai adalci da inganci, da yayata fasahar AI don amfanar dukkan bil-adama. (Ibrahim Yaya)