logo

HAUSA

Abubakar Sadiq Ibrahim: Na zo da niyyar ganin yadda kasar Sin take bunkasa tattalin arzikinta

2024-02-06 15:53:21 CMG Hausa

Abubakar Sadiq Ibrahim, dan asalin Adamawa ne daga tarayyar Najeriya, wanda ya dade yana karatu a kasar Sin. A halin yanzu yana karatun digiri na uku a jami’ar koyon fasaha ta BIT dake Beijing.

A zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar ya bayyana yadda ci gaban kasar Sin ya burge shi, musamman a fannonin da suka shafi tattalin arziki da kimiyya da fasaha, gami da yadda yake jin dadin mu’amala da abokan karatu da malamansa a kasar Sin.

A karshe Abubakar ya kuma bayyana burin da yake son cimmawa. (Murtala Zhang)