logo

HAUSA

Bikin bazara da ke fadada a duniya alama ce ta mu'amala da fahimtar juna tsakanin wayewar kan kasar Sin da wayewar kai daban-daban

2024-02-06 20:10:55 CMG Hausa

A karshen shekarar da ta gabata, babban taron MDD karo na 78 ya zartas da kudurin sanya bikin bazara, wato sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a matsayin lokacin hutu na MDD.

Yayin da bikin bazara na shekarar Loong wato Dragon a Turance ke karatowa, a karon farko, hukumar kula da samar abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO), da hedkwatar MDD dake birnin Vienna, sun gudanar da bukukuwa don murnar sabuwar shekarar kasar Sin a hukumance.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi na yau Talata 6 ga wata cewa, bikin bazara "lokacin Sinawa ne" da dubban iyalai ke haduwa, kuma lokacin hutu ne da duk duniya ke murnarsa.

Jami’in ya kara da cewa, a halin yanzu, kusan kasashe 20 na duniya sun ayyana bikin bazara a matsayin lokacin hutu a hukumance, kuma kusan kashi daya bisa biyar na al'ummar duniya ne ke murnar bikin bazara ta hanyoyi daban-daban. Bikin bazara ya gaji manufofin al'adun gargajiyar kasar Sin na zaman lafiya da jituwa. Bikin bazara da ke fadada a duniya wata alama ce ta mu'amala da fahimtar juna tsakanin wayewar kan kasar Sin da sauran wayewar kai daban-daban, da kuma kasancewar al’adu masu kyau iri daban daban tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)