logo

HAUSA

An rantsar da Nangolo Mbumba a matsayin shugaban Namibia na hudu

2024-02-05 11:23:26 CMG Hausa

A jiya ne, tsohon mataimakin shugaban kasar Namibiya Nangolo Mbumba, ya yi rantsuwar kama aiki a Windhoek, babban birnin kasar a hukumance a matsayin shugaban kasar na 4, bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Hage Geingob da safiyar jiyan yana da shekaru 82.

 An haifi Nangolo Mbumba ne a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1941, ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban kasar Namibia na biyu tun daga shekarar 2018. Mamba mai kwazo a kungiyar SWAPO, Mbumba ya rike mukamai da yawa, inda ya jagoranci ma'aikatu daban-daban a Namibiya.

A cikin wata sanarwar da fadar shugaban Namibiya ta fitar jiya da safe, Mbumba ya bayyana cewa, a cikin tsananin bakin ciki da nadama ina sanar da ku cewa, Allah ya yiwa shugaban kasar Namibia, masoyinmu Dakta Hage G. Geingob ya rasuwa yau Lahadi 4 ga Fabrairu 2024 da misalin karfe 12 da mituna 4 na safe a Asibitin Lady Pohamba inda likitocin sa kekula da shi.

Ya ce, Geingob, firaminista na farko kuma shugaban Namibiya na uku, ya yi gwagwarmaya matuka, daga mai fafutukar yaki da nuna wariyar launin fata zuwa wani babban jigo a tsawon rayuwarsa. An rantsar da Geingob a matsayin shugaban Namibiya a ranar 21 ga Maris din shekarar 2015, an kuma sake zabensa na tsawon shekaru biyar a shekarar 2019. Ya rike mukamin firaminista daga shekarar 1990 zuwa 2002 da kuma shekarar 2012 zuwa shekarar 2015, baya ga wasu muhimman mukaman minista da sauran mukamai da ya rike. (Ibrahim Yaya)