logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi jimamin rasuwar shugaban kasar Namibiya Hage Geingob

2024-02-05 19:50:08 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana alhinin rasuwar shugaba Hage Geingob na kasar Namibiya, inda ta mika ta'aziyya ga gwamnati da jama'ar kasar, da ma 'yan uwan marigayin.

A jiya Lahadi 4 ga wata ne, gwamnatin kasar Namibiya ta sanar da rasuwar shugaban kasar Hage Geingob sanadiyyar rashin lafiya.

Da yake mika ta’aziyya a madadin kasar Sin yayin taron manema labarai na yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya bayyana shugaba Geingob a matsayin tsohon abokin al'ummar kasar Sin wanda aka dama da shi wajen kafawa tare da raya bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Namibiya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa wajen sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce a wannan lokaci na jimami, jama'ar kasar Sin za su tsaya tsayin daka tare da al'ummar Namibiya.

Har ila yau yayin taron manema labaran na yau, ya tabo batun da farmakin da sojojin Amurka suka kai kan kasashen

Syria da Iraki a ranar 3 ga wata, inda ya bayyana cewa, Syria da Iraki kasashe ne masu cin gashin kansu, kuma kasar Sin na adawa da matakan da suka saba wa kundin tsarin mulkin MDD, da cikakken ‘yancin mulkin kai da tsaron kasashe. (Mai fassara: Bilkisu Xin)