logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kaddamar da shirin kawo karshen karancin abinci mai gina jiki

2024-02-05 10:48:28 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Nasarawa dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta kaddamar da wani shiri na hadin gwiwa tsakanin ma’aikatu domin samar da abinci mai gina jiki da zumma dakile yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a daukacin kananan hukumomin jihar 13.

A lokacin da yake kaddamar da shirin tare da wani littafi da zai haske yadda za a tafiyar da shirin, gwamnan jihar ta Nasarawa Alhaji Abdullahi Sule ya ce, an dauki wannan mataki ne bisa la’akari da yadda matsalolin karancin abinci mai gina jiki ke ci gaba da kawo illa ga lafiyar al’ummar jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gwamnan na jihar Nasarawa ya ce, manufar wannan shiri da aka kaddamar a kan abinci mai gina jiki shi ne domin ya kasance jagora da tsarawa tare kuma da aiwatar da tsare-tsare a kan yadda ma’aikatun gwamnatin jihar za su shigo ka’in da na’in wajen tabbatar da wadatuwar abinci mai gina jiki a jihar.

A jawabinta yayin bikin, kwamishiniyar kudi da kasafi da kuma tsare-tsare ta jihar Hajiya Munira Abdullahi cewa ta yi, “Umarnin baya-bayan nan da aka baiwa ofishin shugaban ma’aikata na jihar wajen kirkirar sashen lura da abinci mai gina jiki a dukkannin ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnatin jihar, wata ’yar manuniya ce dake alamanta cewa ana kan turbar nasara.”

A yayin kaddamar da shirin, wakiliyar asusun yara na majalissar dinkin duniya Madam Jane Amwe ta yabawa gwamnatin jihar tare da alkawarin cewa, asusun na UNICEF zai bayar da dukkannin hadin kan da ya kamata wajen samun nasarar shirin a jihar ta Nasarawa. (Garba Abdullahi Bagwai)