logo

HAUSA

An gudanar da bikin al’adu a Alkahira domin murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sin

2024-02-05 10:06:39 CMG Hausa

A yammacin ranar Asabar ne aka gudanar da wani biki a Alkahira na kasar Masar domin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da za ta fada a ranar 10 ga watan Fabrairun bana.

Bikin wanda cibiyar al’adun kasar Sin dake birnin Alkahira ta dauki nauyinsa, ya nuna wasannin kade-kade da raye-rayen na al’adun Sinawa. Matsan Masar su ma sun shiga shagalin a cikin tufafin gargajiya na Sinawa, sun rubuta sunayensu da Sinanci, sun ci abinci Sinawa, kuma sun  shiga ayyukan al’adu da suka hada da zane-zane, da yanka takarda da almakashi, da dandana shayi.

Da yake jawabi a wajen taron, darektan cibiyar kuma mai kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin kasar Sin dake Masar Yang Ronghao, ya bayyana cewa, Masarawa na kara sha'awar halartar sha’anin al'adun kasar Sin, wanda ya alakanta shi da bunkasar dangantakar dake tsakanin Sin da Masar a ‘yan shekarun nan.

Cibiyar za ta ci gaba da inganta mu'amalar al'adu da fahimtar juna tsakanin Sin da Masar, a cewar sa. (Yahaya)