logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon ta’aziyya ga sabon shugaban kasar Namibia

2024-02-05 20:37:36 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Namibia Hage Geingob ga sabon shugaban kasar, Nangolo Mbumba.

A madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin da ma shi kansa, shugaba Xi ya bayyana alhinin mutuwar Hage Geingob tare da mika ta’aziyya ga ‘yan uwansa da ma al’ummar kasar ta Namibia. (Fa’iza Mustapha)