logo

HAUSA

An kammala bita ta hudu ta shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin

2024-02-04 21:46:13 CMG Hausa

Yau Lahadi 4 ga wata, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice ya cimma nasarar gudanar da bita ta hudu ta shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2024, inda aka kara amfani da fasahohin zamani.

Bayan maimaitawa sau da dama da aka yi, ana iya gudanar da shirye-shiryen yadda ya kamata, hakan ya sa shagalin ke cike da yanayi mai kuzari. (Mai fassara: Bilkisu Xin)