logo

HAUSA

Yawan jarin da kasar Sin ta zuba a ketare a bara ya karu kamar yadda ya kamata

2024-02-04 15:07:05 CMG Hausa

Alkaluman kididdga da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar yau Lahadi sun bayyana cewa, a shekarar bara, jimilar jarin da Sin ta zuba a kasashen waje kai tsaye a shekarar bara, ya kai fiye da RMB yuan triliyan 1.04, wadda ya karu da kashi 5.7 cikin 100 bisa makamancin lokaci na shekarar 2022. Adadin ya alamta cewa, hadin gwiwar zuba jari da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen waje ya bunkasa kamar yadda ake fata.

Alkaluman da abin ya shafa sun nuna cewa, a shekarar bara, jarin kai tsaye wanda bai shafi hada-hadar kudi ba da kasar Sin ta zuba a kasashen waje, ya kai RMB yuan biliyan 916.99, wanda ya karu da kashi 16.7 bisa dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022, wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 130.13, wato ya karu da kashi 11.4 cikin 100 bisa makamancin lokaci na shekarar 2022. Kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin kai tsaye da bai shafi hada-hadar kudi ba a kasashen dake bin shawarar "Ziri daya da hanya daya", wanda ya kai RMB yuan biliyan 224.09, wanda ya karu da kashi 28.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 31.8, wato ya karu da kashi 22.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2022. (Safiyah Ma)