logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da ka’idojin cinikayyar hayakin Carbon

2024-02-04 21:58:23 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya rattaba hannu kan dokar da majalisar gudanarwar kasar ta ayyana, wadda ta gabatar da sabbin ka’idojin cinikayyar hayakin Carbon

Ka’idojin za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, wadanda ke da nufin samar da wani tsarin doka na tafiyar da kasuwar cinikayyar hayakin Carbon domin tabbatar da ingancinta da sauran manufofi masu ruwa da tsaki.

Kasar Sin na da niyyar kai wa matsayin koli na fitar da hayakin Carbon zuwa shekarar 2030, sannan ta daidaita hayakin da abubuwan dake iya zuke shi zuwa shekarar 2060. (Fa’iza Mustapha)