logo

HAUSA

Shugaban Senegal ya sanar da dage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairu

2024-02-04 09:59:53 CMG Hausa

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanar da dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An bayyana sanarwar ce a wani sakon da aka watsa wa al'ummar kasar ta gidajen rediyo da talabijin, sa'o'i kadan kafin fara yakin neman zabe da tsakar daren ranar Lahadi.

A jiya ne dai, majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar neman dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairu, zuwa tsawon watanni shida.

'Yan takara 20 ne majalisar tsarin mulkin kasar ta tantance, wadanda za su fafata a zaben. Ko da yake shugaba Macky Sall ya yanke shawarar kin tsayawa takara karo na uku. (Ibrahim Yaya)