logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa’adin shekaru uku domin farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta dake jihar Kogi

2024-02-04 09:07:02 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin nan da shekaru uku masu zuwa kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta dake jihar Kogi a arewa ta tsakiyar Najeriya zai dawo da aiki gadan- gadan.

Ministan ma’aikatar bunkasa harkokin tama da karafa na kasar Alhaji Shu’aibu Audu ne ya tabbatar da hakan ga taron manema labarai a birnin Abuja. Ya ce, a yanzu haka tuni ma’aikatar ta ci gaba da shirye-shiryen jinginar da kamfanin domin hanzartar farfadowarsa cikin hanzari kamar yadda shugaban kasa ya yi umarni.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya ce, da zarar kamfanin na Ajaokuta ya dawo aiki, za a yi maganin kaso 90 na dogaro da kasar take yi wajen shigo da karafa daga waje, inda ya yi bayanin cewa gwamnatoci da dama a baya sun yi kokarin farfado da kamfanin da ya daina aiki shekaru 45 da suka gabata, amma yawan adawa da yunkuri ya dakile kokarin na gwamnatocin.

Alhaji Shu’aibu Audu ya ci gaba da bayanin cewa yana da tabbacin yunkurin wannan gwamnati zai iya kaiwa ga gaci saboda da damuwar da shugaban kasa Tinubu ke da ita ga sha’anin fasahar kere-kere a cikin kasar.

Ya ce wa’adin shekaru uku da gwamnati ta diba tabbas ya isa kamfanin karafan na Ajoakuta ya fara sarrafa karafa da sauran injuna.

Domin samun cimma wannan buri, a cewar ministan, ana neman tsabar kudi har dala biliyan 5, kuma an yi hasashen cewa za a sami gurabe dubu dari 5 na aikin yi tare kuma da samun dala biliyan 10 a matsayin kudin shiga.

“Ha’ila yau kuma muna tattaunawa da wasu masu saka jari daga kasashen waje domin su zo su sake kafa wani sabon kamfanin sarrafa karafa.” 

A kalla dai kamar yadda ministan ya fada, Najeriya na kashe sama da dala biliyan 4 a kowacce shekara wajen shigo da karafuna daga waje. (Garba Abdullahi Bagwai)